Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi birnin New York kasar Amurka ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya (UNGA77).
A bisa jawabin da Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar ranar Asabar, tuni an fara shirye-shiryen taron gangamin, rahoton AriseTV.
Adesina ya bayyana cewa abubuwan da za’a tattauna a taron gangamin sun hada da rikicin Rasha da Ukraine, sauyin yanayi, annobar Korona, da makamashi. Shugaba Buhari zai gabatar da nasa jawabin ranar Laraba, 21 ga Satumba, 2022.
Ya kara da cewa Buhari zai halarci wasu taruka da ganawar diflomasiyya da shugabannin duniya, yan kasuwa, da kungiyoyi.
Shugaban zai samu rakiyar uwargidarsa, Aisha Buhari, da wasu gwamnoni, da ministoci da kuma manyan jami’an gwamnati sa.
Ya ce Buhari zai dawo Najeriya a ranar Litnin, 26 ga Satumba.