Faduwar fan din ingila ya daga darajar kudaden afuruka

Darajar cedi din Ghana na daga cikin kudaden kasashen Afurka da suka fadi

Mintuna 24 da suka wuce
A daidai lokacin da darajar Fan din Ingila ta karye, su kuwa kudaden wasu kasashen Afirka tagomashi suka samu, inda darajarsu ta dan farfado.

A ranar Litinin, darajar fan din ta fadi da kashi 4, idan aka kwatanta da dalar Amurka a kasuwannin Asiya, darajar Shilling din Kenya ya farfado da 0.15, kan fan guda.

A dayan bangaren kuma, an dara a wasu kasashen Afirka, inda darajar kudin Zambia kwacha, da pula na Botswana, da cefar kasashen Afurka su ma sun samu tagomashi.

Sai dai, darajar kudaden Afirka ta Kudu rand, da naira ta Najeriya lamarin ba mai dadi ba ne, saboda sun kara faduwa kasa warwas.

Wannan rana na zuwa ne daidai lokacin da wasu kasashen Afirka suka fuskanci asarar faduwar darajar kudaden idan aka kwatanta da dalar Amurka da fan din Ingila.

Cedin Ghana shi ya fi kowanne karyewa, ya yi faduwar da ba a a taba gani ba cikin shekaru da dama, tun farkon shekarar nan ta yi kasa da kashi 40 idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Cedin ya kara yin kasa da kashi 20 kan fan din Ingila a dai wannan shekara da muke ciki. Amma cedi ya dan yi sama kadan da kashi 10.83 da safiyar ranar Litinin.

“Kasashe na fadi tashi kan farfado da tattalin arzikinsu, musamman ganin kayan da suke fitarwa sun ninka wadanda ke shiga kasashen,’’ in ji Richmond Frimpong, mai sharhi kan lamura a Ghana.

Wannan ya kara janyo bukatar kudaden kasashen waje, da tashin tsadar kayayyaki.

Me ya janyo faduwar darajar fan?
Darajar fan din Ingilar ta fadi a kasuwar duniya, daidai lokacin da gwamnati ta sanar da Karin kudin haraji da ba a taba gani ba cikin shekaru 50.

Fan ya fadi da kusan kashi 1.03 da safiyar Litinin, amma ya dan dago kafin faduwar rana da kashi 1.08.

Sakataren baitil malin Birtaniya, Kwasi Kwarteng ya yi alkawarin rage haraji kari akan fan biliyan 45 da ya sanar a ranar Juma’a.

Masu zuba hannun jari na kasashen Duniya, na saye da sayar da hajarsu da kudaden waje. Manufar ita ce samun riba, saboda za su sayi kudaden masu daraja.

Darajar fan din ta fadi saboda masu zuba jari na saída ita, saboda rashin tabbacin shirin gwamnatoci da ke nuku-nuku, In ji Jabe Foley na Rabobank.

“Sun damu matuka kan sanarwar gwamnati na rage kudin haraji kuma ba lallai su ba da cikakken tallafinsa ba,” in ji ta.

Wannan na daga cikin dalilan da ya tilastawa gwamnatoci cin bashi.

Hakan zai janyo cin bashin makudan kudade, a daidai lokacin da bankin Ingila zai fara saida wasu daga cikin basukan gwamnatin.

Darajar dalar Amurka da fan sun dan farfado a makwannin da suka gabata, to amma na dan lokaci baya sanar da kwarya-kwaryan kasafin kudi domin farfado da dala.

A farkon watan Satumba dalar ta fadi da kashi 1.35, karon farko da ta yi kasa da 1.14, cikin shekaru 40.

Hakan na faruwa sakamakon tashin farashin makamashi da sauran kayayyaki, da ke ci gaba da sanya tattalin arzikin duniya cikin garari.

An dade ba a ga tashin farashin kayan abinci cikin sauri ba cikin shekaru 40, farashin makamashi da fetur ma ba a cewa komai.

A bana, darajar fan karye fiye da dalar Amurka da sauran kudade.

Ita ce faduwa mafi muni cikin shekara da ka fuskanta tun bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai a shekarar 2016.

Ana amfani da darajar kudi a kasuwar musayar kudade, ta hanyar saye da sayarwa.

Wasu abubuwan
Akwai kuma abubuwa da dama da suka hada da;

Tattalin arziki: Bunkasar tattalin arziki na sanya darajar kudin kasar ta samu tagomashi, saboda wasu kasashe za su zuba jari a ciki, za su bukaci kudin kasashen domin hakan, hakn zai sanya bukatar ta karu.

Adani: Idan bankin Ingila ya kara kudin ruwa, hakan zai ja hankalin masu zuba jari ko ajiyar kudade, su kara azamar bukatar fan din Ingila.

Farashi: Idan kayan da Birtaniya ke samarwa sukai arha fiye da na wasu kasashe, ‘yan kasuwa daga ketare za su bazama domin bukatar kudin fan domin saya. Wannan zai sanya darajar kudin ta karu

Harkokin kudin gwamnati: Halin da bankin gwamnati ke ciki, da abin da ke kasa, da bashin da ake bi, ka iya shafar darajar kudi.

Hasashe: Tsadar kudin, da saye da sayarwa da hasashen da ake yi watakil darajar ta karu, na sanya mutane hadamar saye domin cin riba nan gaba.

Abin lura shi ne, tsahon wane lokaci za a dauka darajar kudin na faduwa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments