Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin cikin gida da zai duba sabanin da ake samu tsakanin kamfanin NNPCL da kwamitin FAAC.
Rahoto ya fito daga The Cable cewa shugaban kasa ya amince da wata takarda daga NNPC Limited domin abin da ya jawo kamfanin bai sa kudi a asusun FAAC.
Wata majiya ta tabbatar da NNPCL ta bukaci a gudanar da bincike na musamman domin gano hakikanin abin da ya sa kamfanin baya kawo kudi a duk wata.
Wasu manya sun fadawa Shugaban kasa abubuwa da-dama tun da ya shiga ofis cewa NNPC Limited ya ki saka kudi a cikin asusun tarayya.
Saboda ana so a san gaskiyar lamarin, shugabannin NNPC Limited sun rubutawa Shugaban kasa takarda domin ya yi bincike game da lamarin.
Mai girma shugaban kasa ya yi na’am da hakan, ya kafa wani kwamiti domin ya yi bincike a kai.
Kamfanin man ya na ikirarin ya na bin gwamnatin tarayya bashin fiye da Naira tiriliyan 2.4 a sakamakon tallafin fetur, wutar lantarki da sauransu.
Leadership ta ce kwamitin zai fara yin zama ranar Juma’a a ma’aikatar tattalin arziki a birnin tarayya Abuja.