Hukumar tsaron DSS ta Najeriya ta ce jami’anta sun damke wasu ‘yan ta’adda da suka kitsa kai harin ta’addanci kusa da fadar mai martaba Ohinoyi na masarautar Igbira da ke yankin karamar hukumar Okene a jihar Kogi a daidai lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ziyarar aiki a yankin.
Sanarwar da kakakin hukumar ta DSS a Najeriya Dr. Peter Afunyaya ya tura wa sashen Hausa na Muryar Amurka na cewa jami’an tsaron sun cafke Abdulmumin Ibrahim Otaru da kuma ake kira Abu Miqdad, da Sa’idu Sulyman da ake zarginsu da hannu a harin.
Dr. Afunyaya ya ce Abu Miqdad ya yi kokarin arcewa a lokacin da aka yi kokarin cafke shi, dalili kenan da ya sa jami’an tsaron suka harbeshi da bindiga inda ya sami rauni a kafarsa ta hagu. A halin yanzu ana yi mashi jinya a wani asibiti.
Binciken farko da hukumar ta DSS ta gudanar ya nuna cewa Abu Miqdad shi ne babban kwamandan kungiyar ISWAP da ya kitsa kai harin ta’addanci kan wani ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Okehin a jihar Kogi, inda mayakan suka kashe wani Sufetan ‘yan sanda mai suna Idris Musa sannan suka yi awon gaba da bindigogi kirar AK 47 guda biyu.
Bayan haka shi ne kuma ya jagoranci harin da aka kai gidan gyaran hali da ke Kuje a Abuja da kuma wani hari da aka kai kan wani kamfanin ‘yan kasar Indiya da ke Ajaokuta duk a jihar Kogin, inda suka yi garkuwa da Indiyawa uku kana suka kashe mutane biyar, ciki har da ‘yan sanda uku.
Abu Miqdad ya zama kasurgumin dan ta’adda da ke jagorantar satar mutane a jihohin Kogi da Ondo, a cewar hukumar DSS. Ta kuma tabbatar da cewa zata ci gaba da aiki tukuru da sauran jami’an tsaro don tabbatar da samar da ingantaccen tsaro a cikin kasar.