Fitacciyar tauraruwar fina-finan Indiya Priyanka Chopra ta bayyana dalilan da suak sa ta fice daga masana’antar shirye fina-finan ƙasar ta Bollywood.
Yayin da ta bayyana a wani shirin podcast na Amurka, Priyanka Chopra ta ce ba ta jin ɗaɗin yadda ake cusa harkokin siyasa a masana’antar shirya fina-finan ƙasar.
Sannan kuma ta ce ba ta jin dadin aikin da take yi a masana’antar.
Priyanka Chopra ta yi magana kan batutuwa da dama a shirin na podcast, ciki har da ƙaurarta daga masana’antar Bollywood ta Indiya zuwa Hollywood ta Amurka inda ta yi wasu fina-finan.
Ta kuma yi bayanin yadda ta bar Indiya tare da fara zama a Amurka, da yadda labarin soyayyarta da mijinta mawaƙi Nick Jonas.
A shekarar 2018 ne Chopra ta auri mawaƙi kuma tauraron fina-finan Amurka Nick Jonas, inda suka ci gaba da zama a Amurka, inda a shekarar da ta gabata kuma ta haihu.