Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji.Dr.Nasir Ado Bayero tare da Mai Girma Gwamnan Jahar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islamis Sun Kaddamar Bikin Bada Tallafi Karatu na Masarautar Wanda Gwamnatin Jahar Kano Tabayar a Safiyar yau Litinin a Fadar Mai Martaba Sarkin Bichi..!!!
Bikin yasamu Hallartar Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jahar Kano Dr.Nasir Yusuf Gawuna Kuma Dan Takarar Gwamnan a Tutur Jamiyyar Apc da Shugaban Jamiyyar Apc Na Jahar Kano Alhaji.Abdullahi Abbas da da Kwamishinoni da Mai Girma Dan Majalisar Tarraya Mai Wakiltar Karamar Hukumar Bichi Hon.Abubakar Kabir Abubakar da Takwaransa na Karamar Hukumar Tsanyawa da Kunchi Engr.Sani Bala da Mai Girma Dan Majalisar Jaha Mai Wakiltar Karamar Hukumar Bichi Hon.Lawan Shehu da Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Bichi Farfesa Yusuf Mohammed Sabo da Sauran Jamian Gwamnati Hakimai Dagatai Da Masu Unguwanin Dalibai Dakuma Sauran Manya Manya Yan Siyasa Daga Dake Fadin Masarautar Bichi..!!
Daga wakilin aksammedia B.imam
A Jawabinsa Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji.Dr.Nasir Ado Bayero ya Godewa Mai Girma Gwamnan Jahar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Bisa Bada Wannan Tallafi Dayayi yaja Hankalin Daliban Dasu Dage Wajan Neman Ilimi yayi Addu’ar Allah Yakara Yimasu Jagora.