Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya taimaka wajen nasarar jam’iyyar APC da Bola Tinubu a zaɓen shugaban kasan 2023
Umahi ya faɗi haka ne ranar Litinin a jihar Ribas lokacin kaddamar da makarantar Sakandiren al’umma da aka sabunta a Okoro-nu-Odo, ƙaramar hukumar Obio-Akpor.
Umahi, babban bakon da Nyesom Wike ya gayyata, ya ce Ayu ya taimaka wa Tinubu da APC suka ci zaɓen shugaban kasa ta hanyar ƙin sauka daga shugaban PDP.
Gwamnan Ebonyi ya ce zai matuƙar wahala APC ta samu nasara da ace Ayu ya amince da buƙatar gwamnonin G-5 karkashin Wike, kamar yadda PM News ta ruwaito.