Ana sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da jami’an tsaro biyo bayan gargadin da manyan ƙasashen duniya suka yi na yiwuwar kai hare-haren ta’addanci ƙasar.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafafen yada labarai Malam Garba shehu ya fitar, ya ce a yayin ganawar shugaban ƙasar zai saurari bayanai daga manyan hafsoshin tsaron, tare da ƙara ƙaimi a fannonin da ke buƙatar kulawa.
ƙasashen kamar Amurka, da Birtaniya, da Canada sun gargaɗi ƴan kasarsu da su yi taka-tsantsan saboda sun samu bayanan da ke cewa za a kai hare-hare a ƙasar, musamman ma a Abuja, babban birnin ƙasar.
Kasar Amurka a nata ɓangaren ta buƙaci ma’aikatan ofishin jakadancin ƙasar a Najeriya su fice daga Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shawarci hukumoin tsaron ƙasar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka tsantsan da kula kan sha’anin tsaro, amma kuma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a guji tayar da hankula.
Kazalika shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin cewa gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro.