Real Madrid ce ke kan gaba cikin kungiyoyin da ke son daukar Jude Bellingham, dan wasan tsakiya mai shekara 19 daga Borussia Dortmund a kakar wasa mai zuwa. (Fichajes – in Spanish)
Frenkie de Jong zai zamansa a Nou Camp duk da hasashen da ake yi na alakanta shi da Manchester United. Dan wasan tsakiyan mai shekara 25 ya ce ba zai saurari wani tayi ba a watan Janairu mai zuwa. (Sport – in Spanish)
Juventus na son sayo Sergej Milinkovic-Savic, dan wasan takiya dan kasar Serbia mai shekara 27 daga Lazio.
Kungiyar na kuma son dauko Alessandro Bastoni mai shekara 23 daga Inter Milan baya ga shawo kan Antonio Conte ya bar Tottenham domin ya horas da ‘yan wasan kungiyar. (Calciomercato – in Italian)
Sai dai mataimakin shugaban Juventus Pavel Nedved ya ce kungiyar ba ta da shirin sauya kocinta Max Allegri domin yana aikinsa yadda ya kamata. (DAZN – in Italian
Nottingham Forest da Tottenham da West Ham da kuma Marseille sun bayyana shirinsu na sayan Ruslan Malinovskyi, dan wasan tsakiya na Atalanta mai shekara 29. (Calciomercato – in Italian)
Atletico Madrid ta ki amincewa da tayin euro miliyan 100 da Bayern Munich ta yi kan Joao Felix, dan wasan gabanta dan Portugal kuwa mai shekara 22, zuwa kakar wasa mai zuwa. (Marca – in Spanish)
Real Madrid na shirin mika tayin tsawaita kwantiragin dan wasanta na tsakiya Marco Asensio, yayin da kwantiraginsa ta kusa kawo karshe. (Marca – in Spanish)