Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin saka hannu kan dokar da za ta bai wa matan kasar damar zubar da ciki, matukar jam’iyyarsa ta ci gaba da samun rinjaye a majalisa a shekarar mai zuwa.
ista Biden ya ce da zarar suka lashe zaben rabin wa’adi, zai yi kokarin ganin cewa an sake dawo da hukuncin baya na Roe vs wade, da ya ba da damar zubar da ciki.
A cikin watan Yuni ne kotun kolin Amurka ta soke damar, lamarin da ya haifar da rabuwar kai a kasar.
Yan Demokrats na goyon bayan yancin mata na su yi yadda suke so da jikinsu ciki hadda iko da haihuwa ko zubar da ci kinsu.