Yau ake cika kwanaki 100 da fara yakin Rasha a Ukraine, yakin da ke matsayin mafi muni da nahiyar Turai ta gani a Gomman shekaru, wannan na zuwa a dai dai lokacin da shugaba Volodomyr Zelensky ke cewa yanzu haka kashi 20 na kasar na hannun Rasha.
Da sanyin safiyar ranar 24 ga watan Fabarairu ne jiragen Sojin Rasha suka fara luguden wuta ta sama a biranen Ukraine da dama, wanda ya faru kwanaki kalilan bayan wani atisayen Soji da Moscow ta gudanar na hadin gwiwa da Belarus, haka zalika bayan tsawon lokaci ana zargin kasar da yunkurin mamayar makwabciyarta amma ta na musantawa.
Bayan mabanbantan farmakin na ranar 24 ga watan da shugaba Vladimir Putin ya bayyana da yunkurin kakkabe masu ra’ayin ‘yan Nazi, shugana Volodomyr Zelensky ya ci gaba da zama a birnin Kiev don bayar da kariya ga kasarsa.
A ranar 26 ga wata ne kasashen Turai da Amurka suka hade baki wajen kullewa jiragen Rasha sararin samaniyarsu baya ga kakaba mata takunkumai, yayinda a ranar 27 Putin ya bai wa sashen nukliliyarsa umarnin zama cikin shirin ko ta kwana don barazana ga kasashen da ke kokarin yi masa katsalandan.
Kwanaki 4 bayan kaddamar da yakin ne aka fara zaman farko tsakanin bangarorin biyu wato ranar 28 ga wata inda Rasha ta bukaci tabbatar da Crimea a matsayin mallakinta tare da bata tabbacin cewa Ukraine ba za ta shiga kungiyar NATO ba, yayinda Kiev a na ta bangaren ta nemi ficewar dakarun na Rasha baki daya daga sassanta.
Sai dai dukkanin bangarorin biyu sun gaza samun daidaito kan bukatun a tsawon wannan lokaci wanda ya tilasta ci gaba da yakin.
Shugaba Volodymr Zelensky a jawabinsa gaban ‘yan Majalisu, ya ce yanzu haka kashi 1 cikin 5 na fadin kasar na karkashin ikon Rasha, wato kwatankwacin girman kasar Netherlands.
Zuwa yanzu fararen hula dubu 4 da 34 suka mutu tun bayan fara yakin zuwa yanzu yayinda Sojojin Ukraine kusan dubu 2 suka kwanta dama.
Haka zalika bayanai sun ce akwai mutane miliyan 12 da suka tsere daga matsugunansu don kaucewa hare-haren Rasha.