Allah yayi wa mai girma sarkin Makafin Dan Batta Alhaji Abubakar Isa rasuwa a ranar litinin 31-05-2022
Kafin rasuwar sa ya zanta da wakilin Aksammedia Hassan Umar Gwammaja, inda yaja hankalin Makafin na Dan Batta da sauran makafi da su gujewa mutuwar zuciyar musamman wajan jiran sai wani ya basu
Yace suma mutane ne kamar kowa zasu iya koyon Abubuwan da zasu dogaro da kansu.
Marigayin mai kimanin shekarau 82 a duniya, ya rasu yabar ‘ya ‘ya 6 da jikoki da dama, tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulumci ya tanada a fadarsa dake garin Dambatta, Kofar Gabas
Reporter; Hassan Umar Gwammaja