Masu ruwa da tsaki na gasar Europa sun fitar da ranar Alhamis 20 ga watan uktoba mai kamawa a matsayin lokacin da za a doka kwantan wasan gasar da ba a samu damar buga shi ba tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da takwararta PSV Eindhoven.
A ranar alhamis din wannan makon ne aka tsara za a doka wasan amma mutuwar Sarauniya Ingila Queen Elizabeth ll ya tilasta dage wasan lamarin da ya sanya hukumar da ke kula da gasar gudanar da zama na musamman tare da fitar da lokacin daya kamata a buga wasan a nan gaba.
Sai dai matakin sauya wasan na Europa, kai tsaye zai shafi wasan Arsenal da Manchester City karkashin gasar Firimiyar Ingila wanda bisa jadawali zai gudana kwana daya gabanin wasan na PSV Eindhoven.
Tawagar ta Arsenal karkashin jagoranci mai horarwa Mikel Arteta za ta yi tattaki zuwa Brentford a lahadin karshen makon nan don doka wasanta na gaba.