Wani ginin bene mai hawa hudu a titin Imam Street Uyo, babbar birnin jihar Akwa Ibo ya rufta da mutanen da ba’a san adadinsu ba har yanzu. An tattaro cewa wannan gini ya rufto kan wani ginin daban misalin karfe 6:30 na yammacin Asabar
Shugaban hukumar bada agaji na gaggawa wato NEMA na yankin kudu, Mr Godwin Tepikor, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari,
A cewar Jaridar DailyTrust. kawo yanzu an ceto mutane fiye da hudu daga cikin ginin.