Ana korafi kan rufe rajistar Ƴan Nijar mazauna ƙasashen waje da ke zaune a Najeriya tun a yammacin Asabar bayan cikar wa’adin kwanaki goma sha huɗu da hukumar zaɓen ta ƙayyadene hukumar ta dakatar da yin rajistar.
Ana yin rajistar ne game da zaben cike gurbi na yan majalasar dokokin kasar da za su wakilci ‘yan Nijar mazauna kasashen waje a majalisar dokokin kasar.
Babban birnin tarrayar Najeriya Abuja na daga cikin wuraren da ake rajistar.
To sai dai wasu wuraren kamar Jihar Legas za a ci gaba da yin rajistar a ranar Lahadi da Litinin saboda tsaikon da aka samu na kai kayan yin rajistar a wuraren.
Sakamakon cikar wa’adin yin wannan rajista, jama’a da dama sun yi cirko-cirko a gaban ofishin jakadancin Nijar a Abuja inda suke ta yin ƙorafi kan rashin samun yin rajistar.