Masana sun bayyana muhimmiyar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, a matsayin mai matukar muhimmancin da za ta taimakawa nahiyar aiwatar da ajandunta da ma na duniya, ta hanyar ba matasanta horon fasahohi.
Masanan sun bayyana haka ne yayin wani taro mai taken “Makomar hadin gwiwar Sin da Afrika: taron shugabannin matasa”, wanda ya gudana a ranar Alhamis a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Da take jawabi, ministar kula da harkokin mata da walwalar al’ummar ta Habasha, Ergogie Tesfaye, ta ce taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC da aka kaddamar a shekarar 2000, kyakkyawar dabara ce ta warware matsalar karancin fasahohi da kasashen Afrika ke fuskanta.
A cewarta, hadin gwiwar Sin da Afrika da huldarsu ta diflomasiyya na fadada a bangarorin tattalin arziki da zaman takewa da siyasa, tana mai cewa, bangarorin biyu sun kasance masu toshe duk wani kutse daga wurare daban daban na duniya.
Bugu da kari, ta ce aiwatar da ajandun nahiyar da na duniya, kamar ajandar AU ta shekarar 2063 da ta muradun ci gaba masu dorewa ta shekarar 2030, sun dogaro ne ga karfin fasahohi da ilimin matasa, don haka, muhimmin hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika na tattare da dimbin moriya