Birni mafi girma a Afirka ta Kudu, Johannesburg, da babban birnin kasar, Pretoria, na fuskantar karancin ruwa sakamakon raguwar albarkatun ruwa.
Mondli Gungubele, Ministan Kula da Harkokin Gwamnatin Kasar, ya rawaito cewa ruwan da ke cikin madatsun ruwa a lardin Gauteng na karewa saboda tsananin zafi da kuma karuwar bukata.
Gungubele ya ce yanzu haka an aiwatar da aikin yanke ruwa a sassa daban-daban na kasar musamman a birnin Johannesburg da kuma babban birnin kasar, Pretoria a makonnin da suka gabata.
A cikin bayaninsa, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta, Senzo Mchunu ya bayyana cewa suna neman mafita na dindindin na amfani da ruwa tare da gargadin cewa takunkumin na iya wuce watanni 9.
A gefe guda kuma, masana sun yi gargadin cewa kayayyakin aikin rarraba ruwa na Johannesburg, wanda ya kai kimanin kilomita dubu 1 da 200, ya tsufa sosai.
Wannan matsalar ruwa ya sanya kasar cikin halin tsake me wuya.