Kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers, ta dauki dan wasa mai suna, Musa Adam, daga kungiyar kwallon kafa ta FC Sheshe da ke jihar Kano.
Dan wasan ya rattaba kwantiragi na shekaru biyu tare da Rangers International, bayan taka rawa da ya yi a gasar kwallon kafa ta jihar Kano Tofa Premier, tare da kungiyarsa ta FC Sheshe wacce ta ke taka leda a filin wasa na Mahaha da ke bangaren Sharada da Kofar Na’isa.
Dan wasan zai haɗu da mai horaswa dan asalin jihar Kano, Abdullahi Maikaba a sabuwar kungiyar sa.