Ministan shari’a’ na kasar Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, ya ce ƙasar na shirin daukar matakin halasta yin karuwanci ta hanyar yi wa wata doka gyaran fiska.
Tuni dama Majalisar ƙasar ta amince da wata doka ta halasta ayyukan karuwanci da ministan ya gabatar a watan da ya gabata.
”Dokar na son halasta saye da sayar da kayan jima’i wanda hakan zai rage cin zarafin karuwai,” in ji ministan.
Ya ce an wallafa bukatar hakan a yau Juma’a don jin ra’ayoyin mutane kafin majalisa ta amince da shi.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wata kungiyar kare hakkin karuwai mai suna SWEAT na cewa bayan halasta karuwanci, a yanzu masu sana’ar za su yi aiki da tare da ‘yan sanda domin dakile cin zarafi da ake musu.
Sai dai dokokin da suka haramtawa yara yin karuwanci da kuma safarar su don karuwanci za ta ci gaba da aiki.