Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya janye wa ministocin kasar da mataimakansu alfarmar shan wutar lantarki da ruwan sha kyauta a kasar.
Matakin dai bai yi wa ministocin dadi ba , wadanda talakawan kasar ke kallonsu a matsayin mutanen da ba su damu da halin da talaka ke ciki ba, na yawan daukewar wutar lantarki da tsadar rayuwa.
A wani taron manema labarai da ya gudanar, mai magana da yawun shugaban kasar, ya yaba kan yadda mutane suka bayyana ra’ayoyinsu game da lamarin
Ya ci gaba da cewa za a sauya kundin da ke dauke da hakkokin ministocin ta yadda zai dace da yadda al’ummar kasar ke ji”.