cikin daren da ya gabata na jiyan Lahadi gwamnatin mulkin sojin kasar Mali ta sanar da janyewar daga wannan gungu da ya hada Burkina Faso, Chadi, Mauritania da kuma jamhuriyar Nijar, tare da kawo karshen duk wata alakar aikin soji ko yaki da ayyukan ta’addanci karkashin inuwar wannan kungiya da aka kaddamar tun 2014.
Sanarwar ta yi zargin cewa akwai wata kasa wadda ba mamba ba ce a gungun na G5-Sahel amma kuma take haddasa tarnaki wajen ganin cewa ba ta gudanar da taron kungiyar da aka tsara yi ciikin watan Fabrairun da ya gabata a birnin Bamako ba, wanda a lokacinsa ne ya kamata a danka ragamar shugabancin kungiyar a hannun Mali.
Har ila yau sanarwar wadda ministan tsaron cikin gida kanar Abdoulaye Maiga ya sanya wa hannu ta ce, akwai wata kasa mamba a G5-Sahel da ke adawa da gudanar da taron a Mali saboda dalilai na siyasa