Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA sun kama Dagacin garin Gidan Abba da ke ƙaramar hukumar Bodinga a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, da wasu mutum 10 , saboda zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce an kama shi da hodar koken da sauran wasu muggan ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram 33.491kg.
An dai kama Dagacin mai suna Abubakar Ibrahim, mai shekarar 38, tare da sauran mutanen a filin jirgin sama na jihar Enugu a kan hayarsa ta zuwa ƙasar Sifan iya.