- Ɗan wasan tsakiyar Chelsea da Italia Jorginho, mai shekara 30, na neman ƙarin albashi na £150,000 duk mako kafin ya sa hannu kan sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar. (Evening Standard)
- AC Milan na hanzarta tattaunawa kan sabon kwantiragi da Rafael Leao mai shekara 23 daga Portugal duk da sha’awar da Man U ke nunawa kan ɗan wasan. (Express)
- Ɗan wasan Inter Milan da Slovakia Milan Skriniar, 27, da kuma Leao mai taka wa AC Milan leda na iya sa hannu kan sabbin yarjejeniyoyi da kungiyoyin na Italiya duk da nemansu da Chelsea ke yi. (Evening Standard)
- Chelsea ta nuna sha’awar kulla yarjejeniya da dan wasa Lillie dan Canada Jonathan David mai shekara 22 cikin watan Janairu. (Jeunes Footeux, via football.london
- Wata ƙaramar tawagar magoya bayan Barcelona ta kai kara kotu game da cefanar da Lionel Messi zuwa PSG a 2021. Lauyoyi sun bayyana gaban alkali a kotun tabbatar da adalci ta Turai domin bayyana cewa sayar da Messi mai shekara 35 a lokacin ya saɓa dokokin Turai.(Guardian)
Tsohon dan wasan Arsenal William Gallas ya ce dan wasan gaban Brazil Martinelli mai shekara 21 bai kai ga komawa Real Madrid ba. (TalkSPORT)
A gefe guda kuma, wasu kungiyoyin kwallon kafar Turai na neman Kocin Arsenal amma hankalin tsohon dan wasan ya karkata kacokan kan mukaminsa a kungiyar. (Fabrizio Romano)
Juventus ta na son sayen dan wasan tsakiyar Argentina mai shekara 28, Rodrigo De Paul da ke bugawa Atletico Madrid leda. (Calciomercato – in Italia n)