Ganduje ya siyarwa da dan sa kadarorin gwamnatin kano fiye da guda 100

Gwamnati ta siya Da Darajarta Ta Kai Naira Miliyan 500 A Kan Kuɗi Miliyan 10, Cewar NNPP

…ya siyarwa da ɗan nasa kadarorin gwamnatin Kano sama da guda  ɗari

Rahotanni sun bayyana cewa, Jam’iyyar NNPP a Kano, ta zargi gwamnatin APC ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da siyar da wasu kadarori mallakin gwamnatin jihar.

Zargin wanda ake kallon gwamnatin jihar na siyar da kadarorin ga ɗan gwamna ba bisa ka’ida ba, abin da Jami’ar ta NNPP tace ba zata lamunta ba.

Har ma jami’iyyar ta ce za tayi bincike da tabbatar da hukunci da zarar sun karɓi mulkin Kano a ranar 29 ga watan Mayu.

Jawabin hakan na zuwa ne ta bakin shugaban kwamitin karɓar mulkin jihar Kano na jam’iyyar NNPP Abdullahi Baffa Bichi, yayin wata ziyara da yakai Hukumar Kano State Public Procurement Bureau a yammacin wannan Larabar.

Zargin da ke nuna cewa hukumar na cikin kadarorin gwamnati da aka siyarwa da ɗan gidan gwamna, akan kuɗi kimanin Miliyan 10, duk da cewa darajar hukumar ta kai Miliyan 500, a cewarsa.

Kawo yanzu dai ɓangaren gwamnatin Kano ba su magantu kan wannan zargin da NNPP tayi ba.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments