Najeriya da Maroko na shirin ɗaukar wani muhimmin mataki wajen cika burin gina babban bututun iskar gas na nahiyar Afirka, yayin da ƙasashen biyu ke shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar gwamnatoci a wannan shekarar domin aikin bututun da kudinsa ya kai dala biliyan 25, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana a ranar Litinin.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta tabbatar da cikakken goyon bayan siyasa da kuma dokoki da za su jagoranci aiwatar da wannan gagarumin aiki, wanda ke zama wani babban ci gaba a shirin gina bututun iskar gas na African Atlantic Gas Pipeline. Wannan bututu mai tsawon kilomita 6,900 an tsara shi ne domin jigilar iskar gas daga Nigeria ta ketare kasashen yammacin Afirka zuwa Morocco, sannan daga bisani zuwa nahiyar Turai.
Rahoton ya ce, “Za a rattaba hannu kan yarjejeniyar gwamnatoci kan shirin bututun iskar gas na Najeriya zuwa Maroko mai darajar dala biliyan 25 a wannan shekara,” in ji shugaban hukumar kula da albarkatun mai da ma’adinai ta Maroko.









