Kamfanin Ostiraliya Ya Gano Lithium a Najeriya Bayan Bashi Lasisin Hakar Ma’adinai

Wani kamfanin hakar ma’adinai na ƙasar Ostiraliya, Chariot Resources Limited, ya sanar da gano wani ma’adini mai ɗauke da sinadarin lithium a Najeriya, bayan samun amincewar lasisin hakar ma’adinai guda shida daga Hukumar Rajistar Hakar Ma’adinai ta Najeriya (MCO).

Wannan ci gaba na nuni da wani muhimmin mataki da kamfanin ya ɗauka wajen shiga fannin muhimman ma’adinai a ƙasar, wanda ke da matuƙar tasiri ga tattalin arziki da kuma masana’antu na zamani.

A cikin wata sanarwa, kamfanin ya bayyana cewa Hukumar Rajistar Hakar Ma’adinai ta Najeriya (MCO) ta amince da canja wurin lasisi guda shida gaba ɗaya—wanda ya haɗa da lasisin bincike guda huɗu da kuma lasisin ƙananan hakar ma’adinai guda biyu—daga Continental Lithium Limited zuwa C&C Minerals Limited, wato kamfanin haɗin gwiwa da yake da shi a Najeriya.

Lasison sun shafi izinin bincike a ayyukan Fonlo da Gbugbu, da kuma harkokin ƙananan hakar ma’adinai a aikin Saki, wanda hakan ya ba Chariot cikakken iko kan muhimman kadarorinsa a yankin.

Shanthar Pathmanathan, Shugaban Kamfanin kuma Babban Darakta, ya ce:
“Wadannan amincewa na da matuƙar muhimmanci ga kamfaninmu da kuma masana’antar lithium a duniya baki ɗaya, domin suna nuna shigowar kamfanin lithium na farko da aka jera a kasuwar ASX cikin fannin lithium mai ɗauke da babbar dama a Najeriya. Najeriya na da ma’adinan lithium na pegmatite waɗanda tuni ake samar da spodumene daga cikinsu domin kasuwar China, amma har yanzu ba a yi cikakken bincike a yawancin wuraren ba.”

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments