Kungiyar Kakakin Dala ƙarƙashin jagoranci shugaban ta, Farfesa Aliyu Sulaiman Kantudu ta gudanar da rabon takardun JAMB da horas da daruruwan Dalibai Masu aniyar shiga Jami’o’i ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa ta yadda za su gudanar da jarabawar da ke tunkaro su ta JAMB da UTME.
Kungiyar ta jagoranci rabon takardun JAMB Daga ranakun Asabar da Lahadi inda a ranar Litinin ta gudanar da Bayar da horon ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa a Makarantar GSS Dala da ke Gwammaja ga Ɗalibai
A jawabinsa shugaban kungiyar Farfesa Aliyu Sulaiman Kantudu wanda Injiniya Muhammad Auwalu Sanusi ya wakilta ya ce ƙungiyar ta ga dacewar gudanar da wannan ci-gaba ne domin bunkasa al’ummar ƙaramar hukumar Dala.
“Ya ce wannan shine karo na Uku da ƙungiya ta ke gudanar da Irin wannan tagomashi ga dalibai yan asalin ƙaramar hukumar Dala
Taron ya sami halartar wasu Daga cikin Yan ƙungiyar irin su Dakata Yahaya da kuma wasu Daga cikin iyayen ƙungiyar
A nasu bangaren Wasu daga cikin waɗanda suka Amfana da shirin sun bayyana jin daɗin su tare da yin fatan alkhairi ga daukacin yan ƙungiyar Kakakin Dala









