Fiye da Mutane Miliyan 3.3 Sun Rasa Matsugunansu a Najeriya — NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, National Bureau of Statistics (NBS), a turance ta bayyana cewa mutane 3,381,228 sun rasa matsugunansu a jihohi 14 na Nigeria a shekarar 2023.

Wannan na ƙunshe ne a cikin kundin bayanan Demographic Bulletin na shekarar 2023 da hukumar ta fitar a ranar Talata a Abuja. Kundin ya tattara bayanai daga hanyoyin gwamnati da kuma bincike domin taimakawa wajen tsara da gudanar da bincike.

Rahoton ya nuna cewa jihar Borno ce ke da mafi yawan masu gudun hijira a cikin gida, inda ta kai kashi 50.62 cikin 100, wato mutane 1,711,481. Sai kuma Benue da kashi 11.67 (mutane 394,567), sannan Katsina da kashi 7.23 (mutane 244,380).
Haka kuma, jihohin Gombe, Nasarawa, da Kano sun fi ƙarancin adadin masu gudun hijira, inda suka kai kashi 1.55 (52,383), 0.61 (20,580) da kuma 0.46 (15,549) bi da bi.

Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa hasashen yawan al’ummar Najeriya daga National Population Commission ya kai mutane 221,250,127 a shekarar 2023, wanda ya ƙunshi maza 112,434,239 da mata 108,815,888.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments