Saudiyya da Qatar za su tallafawa Pakistan da zunzurutun kudi har Dala Biliyan Biyar

Kasashen Saudiyya da Qatar sun tabbatar wa Pakistan da tallafin kudi da ya kai kimar dala biliyan 5, domin taimakawa kasar rage matsin lamba kan ajiyar kudaden kasashen waje, yayin da take shirin biyan bashin da ke kanta ga kasashen waje a karshen wannan wata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.

Ana sa ran wannan tallafi zai zo ne a daidai lokacin da Pakistan ke shirin mayar da kimanin dala biliyan 3.5 ga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kafin karshen watan Afrilu, bayan bukatar da Abu Dhabi ta yi na a biya bashin da ake binsa.

Taimakon ya fito ne bayan ganawa da aka yi a Islamabad tsakanin Firayim Ministan Pakistan, Shehbaz Sharif, da Ministan Kudi na Saudiyya, Mohammed bin Abdullah Al-Jadaan, inda suka tattauna hadin gwiwar tattalin arziki da kuma halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki. Mataimakin Firayim Minista kuma Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Ishaq Dar, da Shugaban Sojoji, Janar Asim Munir, sun halarci taron.

Rahoton ya ce Pakistan ta kuma nemi karin tallafi daga Saudiyya, ciki har da tsawaita yarjejeniyar samar da man fetur a matsayin bashi da kuma kara yawan kudaden ajiya na Saudiyya da ke babban bankin kasar. Duk da cewa ba a rattaba hannu kan wata yarjejeniya ba, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ma’aikatun kudin kasashen biyu kan yiwuwar karin taimako.

Ana sa ran wannan tallafi daga Saudiyya da Qatar zai taimaka wa Pakistan wajen daidaita ajiyar kudaden waje, wanda a halin yanzu ya kai kusan dala biliyan 16.4, tare da tabbatar da cewa kasar na iya ci gaba da biyan bukatun kudaden waje har zuwa watan Yuni, duk da karuwar farashin shigo da kaya da kuma tashin hankali a yankin.

Hukumomin Pakistan na kuma ci gaba da tuntubar abokan hulda na kasa da kasa gabanin wasu muhimman tarukan kudi da za a yi a Washington, yayin da suke kokarin samun karin kariya daga hadarin karancin kudaden waje.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments