Iran ta bayyana cewa za ta iya dakatar da aikin ƙara wadatar sinadarin uranium na tsawon shekaru biyar, amma gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ta yi watsi da wannan tayin, tana mai nacewa sai an tsawaita wa’adin zuwa shekaru 20.
Rahotanni daga manyan jami’an Iran biyu da kuma wani jami’in Amurka sun nuna cewa wannan sabani ne ya zama babban cikas a tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu.
Ana dai ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, inda Amurka ke son a dakatar da ƙara wadatar uranium na dogon lokaci domin hana yiwuwar kera makaman nukiliya, yayin da Iran ke ganin shekaru biyar sun isa.
ndtv









