Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta dakile wani farmaki da wasu da ake zargin mambobin ISWAP ne suka kai a Maiduguri babban birnin kasar.
‘Yan Sanda Sun Dakile Farmakin da ISWAP ta Kai Caji Ofis a Magumeri, Borno.
Hoto daga TheCable.ng Asali: UGC Kamar yadda Zagazola Makama, wata wallafa da ta mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi ta bayyana,
Jaridar The Cable tace ana zargin mayakan ISWAP ne suka tsinkayi caji ofis din ‘yan sanda dake garin a tawagar motocin yaki da babura wurin karfe 12:35 na safiyar lahadi.
KARA KARANTA WANNAN ‘Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun yi wa Basarake Yankan Rago a Najeriya
Wata majiya makusanciyar da ta dakile harin tace harin yayi sanadin musayar ruwan wuta tsakanin jami’an ‘yan sandan da ‘yan ta’addan.
Ta kara da cewa, yayin da tawagar ‘yan sandan suka iya dakile farmakin cike da nasara, an harbi wani Bitrus Umaru, ‘dan sanda mai mukamin Sifeta, a ciki da kafarsa ta dama.
‘Yan ta’addan sun yi awon gaba da wata mota kirar Hilux ta sintiri.