Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben 2023, ya yi alkawarin bai wa matasan ƙasar kashi 40 cikin 100 na muƙamai idan ya hau mulki saboda yadda ya ga ƙwazonsu.
Atiku Abubakar, ya bayyana haka ne a baya-bayan nan a wani taro da jam’iyyar ta gudanar a jihar Kaduna.
A yayin taron, dan takarar da PDP, ya yi bayani a kan irin manufofinsa ga matasa a Najeriya baki Da ya.
Muhammad Kadade Sulaiman, shi ne shugaban matasan PDP a ƙasar, ya shaida wa manema labarai cewa, a yayin taron da suka yi a Kaduna, Atiku Abubakar, ya ce da ikon Allah idan har ya hau mulki zai farfado da masaku don samar da ayyukan yi ga matasa a Kaduna da ma sauran jihohi.
Dan takarar shugabancin Najeriyar a PDP, ya ce idan har ka bawa matashi abin yi to ba zai ba da kunya ba in ji shugaban matasan PDPn.
A yayin kaddamar da yakin neman zabensa, Atiku Abubukar, ya bayyana wasu matsaloli da ya ce kasar na fuskanta kamar batun tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya, da shiga matsin rayuwa da al’ummar kasar ke ciki, da kuma batun matsalar tsaro.