Tsohon shugaban kasar Zambiya Edgar Lung yayi kakkausar lafazi ga hukumar binciken kasar

Idan na ci kwabon jama’a ku kai ni kotu – Tsohon shugaban kasa.

Daga Walid Hari.

Tsohon shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya ce a shirye yake ya fuskanci hukunci idan har ya saci sisin kwabo a lokacin mulkinsa.

Lungu ba ya farin ciki da binciken aikata laifi da ake yi masa, da jami’an tsohuwar gwamnatinsa da iyalansa game da zamanin mulkinsa.

Musamman ma lokacin da jami’an gwamnati a ranar Alhamis suka je wani fili da ya mallaka don yin bincike.

Edgar Lungu dai ya kalubalanci shugaban kasar mai ci Hakainde Hichilema ya fara da cire wa kansa rigar kariya don ya wanke kansa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments