Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Hukumar hisbah ta jihar Kano ta gayyaci shahararrun masu yada bayanai a shafin Tiktok domin su tattauna mahimman abubuwan da zasu amfani jihar Kano
Babban kwamandan hisbah sheik Haruun muhd sani ibn sina yace ganin yadda Al”amuran matasa suka karkata akan shafin na tikiok yasa sukaga dacewar su zauna dasu domin tsarkake kalamansu da yadda zasu amfanar da al’umma ba cutardasu ba.
Sheik ibn sina yace garin kano Allah ya albarkaceshi da masana da kuma mutane masu mutunci wadanda taba mutuncinsu tamkar taba mutuncin jihar ne don haka ne yasa suka tattauna don a fahimci manufar hukumar ga masu ta’ammali da shafin wanda bazai ka wo gunaguniba .
Mataimakin kwamanda a bangaren samame malam shehu Tasi’u Isha yace zaman nasu na matsayin aikin sumame amma na lumana wanda baya nufin komai sai kawo gyara ga yan Tiktok din baki daya.
Anasa bangaren shugaban kungiyar yan Tiktok Shafiddeen Bature Kawu yace Al,amarin yayi musu dadi kuma sun gane manufar hukumar ta hisbah kuma dama tun asali aikinsu a shafin baya wuce ilmantar da al’umma.
Ya kara da cewa Zasu isar da sakon hisbah ga sauran yan’kungiyarsu don a gyara Baki daya.matashi Mubarak wanda ya ke yada barkwanci a shafin wanda a sakamakon haka yayi subul da baka a shafin har ya janyo masa hukunci yace sun gamsu da bayanan hisbah bazasu sake yin abin da bazai amfani al’umma ba.