Yan kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, na Jami’ar Tarayya ta jihar Jigawa sun yi zanga-zangan lumana kan biyansu rabin albashi
Malaman jami’o’in sun yi tir da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na neman mayar da su ma’aikatan wucin gadi duba da cewa su cikakkun ma’aikata ne
Dr Bashir Yusuf, shugaban ASUU na FUD ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta biya malaman sauran albashinsu da allawus duba da cewa yajin aikin da suka yi kan ka’ida ne
Shugaban na ASUU a FUD, Dr Bashi Yusuf ya bayyana hakan yayin zanga-zangan, yana mai cewa hakan ya saba dokokin aiki, da dokokin kwadago na kasa da kasa da aikin gwamnati.
Dr Bashir ya yi bayanin cewa malaman jami’o’in ma’aikata ne da aka dauke su aiki na cikakken lokaci wadanda ayyukansu ke da wasu banbance-banbance da wasu ma’aikatan gwamnati masu zuwa aiki karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma.
A cewarsa, koyarwa a jami’a cikakken aiki ne da ya kunshi koyarwa, bincike da ayyukan yi wa al’umma hidimar.
“Ba za a rika biyan mu na wucin gadi ba ko rabin albashi kan yajin aiki da muka yi bisa tsarin doka duk da mun dakatar.”
Kungiyar ASUUn ta FUD, ta yi tir tare da nuna amincewarta da mayar da malaman ma’aikatan wucin gadi kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta biya su cikakken albashinsu da allawus.
Malaman na FUD sun yi tattaki na lumana daga Cibiyar Dalibai zuwa ginin Majalisar Jami’ar rike da takardu masu dauke da rubutu daban-daban don isar da sakonni ga gwamnatin tarayya.