Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Haris da shugabannin kasashen Japan da Korea ta Kudu da Australia da New Zealand da kuma Canada, sun lashi takobin matsin lamba kan Korea ta Arewa bayan sun yi wani zama a yau Juma’a, inda suka tattauna game da sabon gwajin makami mai linzami da Korea ta Arewar ta yi.
Japan ta ce, wannan makamin mai linzami da ke keta sararin samaniyar kasa da kasa, ya dira ne a cikin tekunta, kuma yana da karfin isa tsakiyar Amurka, yayin da Harris ta gana da aminan Amurka na kut da kut kan yadda za su tunkakri barazanar.
Gabanin ganawar wadda suka yi a gefen taron Kasashen Asiya da Pacific a birnin Bangkok, mataimakiyar shugaban Amurkar ta shaida wa manema labarai cewa, sun yi tur da wannan al’amari , kuma suna jaddada kira ga Korea ta Arewar da ta daina haramtattun gwajen-gwajen.
Sabon gwajin na zuwa ne a yayin da hukumomin leken asirin Amurka suka yi amanna cewa, Korea ta Arewar na shirin gwajin makamin nukiliyarta a karo na bakwai.
Shugabannin kasashen dai, sun amince cewa, har yanzu kofar tattaunawa a bude take, sannan sun yi kira ga Korea ta Arewar da ta guje wa duk wata takalar fada tare da koma kan turbar diflomasiya mai ma’ana