Amurka ta buƙaci wasu daga cikin jami’an diflomasiyyarta da iyalansu su gaggauta ficewa daga Abuja babban birnin Najeriya sakamakon fargabar kai harin ta’addanci a birnin.
Ofishin jakadancin Amurka a ke Abujar ya bai wa Amurkawa shawarar kar su yi balaguro duk da cewa babu cikakken bayani kan ainahin irin hatsarin da za a fuskanta.
A ranar Laraba Amurka ta fitar da gargaɗi irin wannan a kasar Afirka ta Kudu. Sanarwar ta bukaci Amurkawa mazauna yankin Sandton na masu kuɗi a birnin Johannesburg su guji shiga taron jama’a a karshen makon nan.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce abin takaici ne a ce Amurka ba ta tuntube shi ba kafin ɗaukar wannan ma takin.