EFCC da Masarautar Gargajiya Sun Yi Alkawarin Hada Kai Wajen Yaki da Cin Hanci
Mukaddashin Daraktan Yanki na Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) a shiyyar Katsina, ACEI Chinedu Ozugha, tare da tawagarsa, a ranar Talata 14 ga Afrilu, 2026, sun kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, CFR.
A yayin ziyarar, Mukaddashin Daraktan Yankin ya sanar da Sarkin game da sabon ofishin hukumar da aka bude a Katsina, wanda zai rika kula da jihohin Katsina da Zamfara. Ya kuma roki Sarkin da ya ba da cikakken goyon baya ga ofishin da kuma hukumar baki daya wajen yaki da laifukan tattalin arziki da na kudi, yana mai jaddada cewa ba za a bar wannan yaki ga EFCC kadai ba.
Ya kara da cewa, kasancewar Sarkin jagora ne na gargajiya wanda muryarsa ke da tasiri kuma jama’a ke girmamawa, akwai bukatar goyon bayansa domin cimma nasarar ayyukan hukumar.
A nasa bangaren, Sarkin Katsina ya bayyana farin cikinsa da bude ofishin EFCC a jihar, tare da yin alkawarin bayar da goyon baya domin tabbatar da nasarar ayyukan ofishin.









