Fitaccen jarumin Nollywood, Niyi Johnson, ya ja hankulan jama’a bayan ya bayyana cikin kayataccen shiga a bikin Ojude Oba na shekarar 2026.
Jarumin ya bayyana cikin shiga ta gargajiya mai kayatarwa wadda ta nuna al’adun Yarbawa da kuma martabar bikin. Shigowarsa cikin salo da kwarjini ya kara wa bikin armashi tare da daukar hankulan mahalarta taron.
Masoya da masu bibiyar harkokin fina-finai sun yabawa Niyi Johnson saboda salon shigarsa da yadda ya nuna alfahari da al’adun gargajiya, yayin da hotuna da bidiyonsa suka bazu a kafafen sada zumunta.
Bikin Ojude Oba na daga cikin manyan bukukuwan al’adu a Najeriya, inda ake nuna fareti, hawan dawaki, da kuma al’adun gargajiya tare da halartar fitattun mutane daga sassa daban-daban na kasar.
Ci gaba da karantawa a sashen sharhi.












