An yabawa gwamnatin jihar Borno bisa sake bude kasuwar dabbobi ta kasa da kasa dake Gamboru da ayyukan masu tada kayar baya ya lalata.
Shugaban kungiyar masu fataucin dabbobi ta kasa Alhaji Mustafa Ali ne yayi wannan yabon a zantawarta da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Mustapha Ali jinjinawa kokarin gwamna Baba Gana umara zulum bisa wannan kokari don bunkasar kasuwanci da cigaban tattalin arzikin jihar dama kasa baki daya.
Ya kuma bayyana farin cikinsa bisa sake bude wannan babbar kasuwa inda yace gwamna Baba Gana umara zulum jajirtaccen gwamna ne wanda ya zamto abin koyi ga sauran gwamnonin Arewacin kasarnan.
Ya kara da cewa gwamnan shine ya baiwa gwamnan jihar Adamawa shawara kan kada ya karawa masu fataucin dabbobi haraji don saukakawa masu karamin karfi dake gudanar da kasuwacinsu a ciki da wajen jihar ya kuma amince da hakan.
Sai kuma Shugaban ya koka kan yadda suka tattara bayanai da Rahotanni kan kisan gillar da ake yiwa yankungiyar su da kuma gallaza musu a wasu daga cikin jihohin kasarnan duk da cewar sun zauna da hukumomin jihohin da masu ruwa da tsaki kan lamarin ciki har aikewa da takarda amma har yanzu ba ta sake zani ba.
Ya kuma koka kan yadda gwamnatin tarayya tayi shakulatin bangaro da alkawarin da ta daukar wa kungiyarsu kan cewa zata biya yayanta da iyalan wadanda suka rasa mazajensu diyya muddin suka dakata daga yajin aikin da suka yi yunkurin shiga watannin baya,wanda har ya zuwa yanzu gwamnatin ta gaza biya.
Don haka yake kiran gwamnatin tarayya kan daure ta shigo cikin lamarinsu ta cikawa yayan kungiyarsu alkawarin data dauka na bayansu diyya Sannan kuma ta tabbata ta takawa kudancin kasarnan birki wajen cin zarafi da gallazawa da suke fuskanta a wuraren kasuwacinsu a fadin kasarnan.
Daga karshe ya yi Kira ga yayan kungiyarsu kan su cigaba da hakurin da suke yi kasancewar Shugabancin kungiyar a matakin jihohi da kasar ma baki daya na ta kokarin shawo kan gwamnatin tarayya ta yadda zata Samar da dokar da zata kare musu mutuncin su tare da kare rayukansu dukiyoyinsu a fadin kasarnan.