Daga Jamila sulaiman Aliyu.
Kungiyar da take kawo gyara tare da samarda dai daito a tsakanin al’umma ta gudanar da taro da mataimakansu dake unguwanni don kaucewa rikici saboda sabanin ra’ayi a zabubbukan dake tafe.
Shugaban kungiyar kwamared usman Abdulhamid yace ganin zabe na karatowa da kayyadadden lokacin dabai wuce kwanaki dari ba ya sanya su yin taro da mataimakansu a unguwanni CPO’S domin kara kaimi akan aikinsu na fadakarwa a tsakanin Al,umma domin samun yin zabe mai kunshe da lumana.
kwamaret usman Abdulhamid yace ta hanyar dakile hatsaniya da zarar an farga za,a samu nasara don Kar,a yi rikici wanda zai kawo nadama sannan idan ya faru duk da ba,a fata a samu nasarar dakatar dashi kafin yakai ga kazanta ko kuma yin kamari.
Sakataren kungiyar, Dakta Sama,ila Joshua Asake, yace sunyi dauraya daga ayyukan da suka gabatar a tarurrukan da suka gabata domin sake fahimtar manufar kungiyar don tunkarar zaben dake tafe