Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026, inda aka amince da jimillar kashe kuɗi na naira tiriliyan 68.32 domin gudanar da harkokin gwamnati a wannan shekarar kasafi.
Haka kuma, shugaban ya sanya hannu kan wata doka da ta tsawaita wa’adin aiwatar da ɓangaren ayyukan raya ƙasa (capital projects) na kasafin kuɗin 2025 daga ranar 31 ga Maris zuwa 30 ga Yuni.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a a birnin Abuja.
A cewar Onanuga, kasafin kuɗin shekarar 2026 ya tanadi naira tiriliyan 4.799 domin kuɗaɗen da doka ta tanada (statutory transfers), yayin da aka ware naira tiriliyan 15.8 domin biyan basussuka.
Haka zalika, an ware naira tiriliyan 15.4 domin kuɗaɗen gudanarwa (recurrent expenditure), sannan naira tiriliyan 32.2 domin asusun raya ƙasa (Development Fund) na ayyukan ci gaba.
Kasafin ya nuna fifiko ga ayyukan raya ƙasa da bunƙasa tattalin arziki, inda kashe kuɗin ayyukan ci gaba ya kai kusan kashi 50 cikin 100 na jimillar kasafin.
Onanuga ya ce wannan tsari na kasafin kuɗi ya jaddada ƙudurin gwamnatin wajen ƙarfafa tattalin arziki da samar da ci gaba mai ɗorewa.








