China Ta Mayar da Martani Mai Zafi ga Trump Kan Batun Iran da Tsaro

Kasar China ta yi kakkausar suka ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump, tare da karyata rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta amince da Amurka kan batun dakatar da bai wa Iran makamai.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Guo Jiakun, ya bayyana cewa babu wata tattaunawa da ta gudana tsakanin China da Amurka kan wannan batu.

“Na na son kawo karshen jita-jitar da ke yawo a yanar gizo da ke cewa China ta amince da Amurka ba za ta bai wa Iran makamai ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Bari in fayyace cewa babu wata irin wannan magana da ta faru. China ba ta tabbatar ko musanta cewa tana bai wa Iran makamai ba.”

Jiakun ya jaddada cewa yarjejeniyoyin tsaro da hadin gwiwar tsaron China lamari ne na ‘yancin kai na kasar, wanda babu wata kasa da ke da ikon tsoma baki a ciki.

“Hadin gwiwar tsaron mu lamari ne na mu kadai. Babu wata kasa da ke da hurumin shiga harkokin cikin gidan China,” in ji shi.
Har ila yau, ya gargadi shugabannin duniya da su rika taka-tsantsan wajen furta kalamai.

“Ya kamata shugabannin duniya su rika zabar kalamansu da kyau kafin su yi magana,” in ji shi.

A karshe, China ta bayyana maraba da matakin da Shugaba Trump ya dauka na rage tashin hankali da kuma bude mashigar ruwa ta Strait of Hormuz.

“China na maraba da matakin da Shugaba Trump ya dauka na rage tashin hankali da kuma bude mashigar Hormuz. Muna nan daram wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya da kuma kare zaman lafiya a yankuna ta hanyar tattaunawa,” in ji Jiakun.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments