Kimanin Watani Uku kenan da Uwar Jam’iyyar APC Ta Kasa Ta Fitar Da Sannawa Cewar Zata Gudanar Da Zabenta Na Kasa
Babbar Jam’iyyar mai mulki a Najireya APC karkashin jagorancin riko da gwamnan jihar Yobe Maimala Buni ta sanya ranar asabara 26 ga watan fabrairun wannan shekara a matsayin ranar da zata gudanar da taron ta na kasa domin, zabar sababin shugabanin jam’iyyar
Ganin lokaci na daf da karatuwa, alamu sun nuna babu alamar shirye-shiyen gudanar da zabe, a wanda ake sa ran yinsa a babban birnin tarayya Abuja
Aksam Media ta ji tabakin wasu jiga-jigan jam’iyyar a nan jihar Kaduna in da suka bayyana rashin masaniyar kin fara shiye-shiyen zabe,
Sai dai wata majiya tace wata kila hakan yana da alaka, da yadda gwamnonin jam’iyyar APC suka nuna, suna son ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma hakan baiyuba sakamakon ya na shirin ta fiya taron Kasashen masu tattalin arzikin man fetir.
By Hassan Umar Gwammaja