Daga Ibrahim sani gama
Kungiyar yankasuwa ta karamar hukumar kabo,ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta zauna da dillalen man fetur da sauran masu ruwa da tsaki a fannin man domin sanun daidaiton da zai kawo karshen wahalar man da ake fama da shi a jihohin kasar nan.
Daya daga cikin jagororin kungiyar Alh Mahmuda zangon kabo,ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake ganawa da manema labarai a nan kano.
Zangon kabo,yace zama da yankasuwar da suke shigo da man yana da mutukar amfani domin jin makasudu da yasa man yake wahalar samu da kuma,tsada a wasu daga cikin gidajen man fetur.
Yace,kamata yayi Gwamnati ta yi wani Abu kasancewar wannan matsala ta shafi fannoni da dama ciki har da kasuwanci,saboda farashin kayayyakin masarufi ya tashi a kasuwanni da kudaden ababen hawa,Wanda ya jayo talakawa suna fuskantar kalubale da yawa.
Mamuda yace zaman shine abin da zai kawo kyakyawar fahinta a tsakanin juna da kuma,samarwa alumma sauki a harkokin rayuwarsu ta yau da kullum.
Haka zalika,ya shawarci alumma kasar nan da su kasance masu gudanar da addu,oin samun sauki akan alamura da suke damunsu,musamman matsalolin rashin tsaro daya zama ruwan dare gama duniya.
Yace Gwamnati tana da rawar takawa ta fannoni da yawa kasancewar itace uwar kowa wadda take da hanyoyin da za ta samarwa alumma abubuwan more rayuwa da sauran kayayyaki da zai iya amfanar su.
Yace,akwai bukatar alumma su rika yiwa su Kansu shugabannin addu,a domin basu kwarin gwiwar aiwatar da ayyukan ci gaba mai dorewa.