Shugaba Buhari Ya aika sakonni ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mai taimaka masa na musamman

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba ya yi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mai taimaka masa na kai da kai a ɓangaren kafafen watsa labaran zamani, Buhari Sallau.

Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito tace mahaifiyar Buhari Sallau, watau Maryam Muhammed, ta rasu tana da shekaru 65 a duniya.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajanta wa hadiminsa, Buhari Sallau, dangane da rasuwar mahaifiyarsa, Maryam Nuhammed .

Mai taimaka wa shugaban kasan kan kafafen watsa labaran zamani, Buhari Sallau, ya yi rashin mahaifiyarsa tana da shekaru 65

A sakon ta’aziyya na musamman da ya aike masa, Buhari ya roki Allah ya gafarta mata ya sa Aljanna ta zame mata makoma

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments