Sakataren Majalisar tsaro ta Iran, Ali Larijani ya ce Ya kamata jama’ar Amurka su sani cewa Duk abin da ya Biyo Trump ne ya fara wannan kasada, kuma su yi taka-tsantsan da sojojinsu
Larijani, ya bayyana cewa ya zama wajibi jama’ar Amurka su fahimci cewa Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ne ya fara abin da ya kira “wannan kasada”, tare da gargaɗin cewa ya kamata su yi hattara da lafiyar sojojinsu.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Larijani ya ce matsayar jami’an Isra’ila da ta Trump ta bayyana a fili asalin abin da ya faru. Ya ƙara da cewa Iran tana rarrabe matsayar ɗan kasuwan da ke nuna adawa da abubuwan ɓarna da wasu ke yi.
Larijani ya jaddada cewa Trump ya kamata ya sani duk wani katsalandan da Amurka za ta yi a cikin wannan lamari na cikin gida zai iya jawo rugujewar yankin gaba ɗaya, tare da lalata muradun Amurka.
Ya sake nanata cewa jama’ar Amurka su fahimci cewa Trump ne ya jefa lamarin cikin wannan hali, kuma su kula da makomar sojojinsu.
Ali Larijani, Sakatare na Majalisar Tsaron Ƙasa ta Ƙoli ta Iran, ta shafinsa na X.









