Mataimakin shugaban Majalisar Tsaron Rasha, Dimitri Medvedev, ya bayyana cewa Rasha na iya kaiwa ga bai wa Iran makaman nukiliya idan har Jagoran Kolin ƙasar ya nemi hakan.
Ya ce akwai yarjejeniyar tsaro tsakanin Rasha da Iran da ke ba da damar irin wannan mataki, yana mai jaddada cewa Rasha ba za ta zauna tana kallo ba idan aka ci gaba da barazana ga Iran.









