Bayan kama Maduro, Trump da Jam’iyar sa sun Fara Fuskantar Bore da suka daga Amurka wa

Wani sabon binciken jin ra’ayi ya nuna cewa matakin da Donald Trump ya dauka na kai hari da sace Shugaban ƙasar Venezuela ya janyo masa gagarumar suka daga yawancin ‘yan Amurka, inda lamarin ya zama abin ce-ce-ku-ce a cikin ƙasar.

Binciken Reuters/Ipsos ya nuna cewa kashi 33% kacal na ‘yan Amurka ne suka amince da harin, yayin da kashi 72% suka nuna damuwa cewa Amurka na iya tsunduma sosai cikin harkokin cikin gida na Venezuela.

Rahoton ya bayyana cewa Trump ya danganta harin da batun kwace man fetur na Venezuela, lamarin da masana ke cewa keta dokokin kasa da kasa ne kuma ba shi da alaka da tsaron kasa na Amurka.

A bangaren siyasa, kashi 65% na ‘yan jam’iyyar Republican sun goyi bayan matakin, amma goyon baya daga ‘yan Democrat da masu zaman kansu ya kasance kadan, abin da ka iya shafar damar Republican a zaben tsakiyar wa’adi.

Binciken ya kara da nuna cewa kashi 30% ne kacal ke goyon bayan tura sojojin Amurka zuwa Venezuela, inda masu sharhi ke cewa jama’ar Amurka sun nuna rashin amincewa da duk wani yunkuri na mamaya ko tsoma baki a wata kasa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments