Masar da Afirka ta Kudu Sun Shiga Jerin Kasashen Afrika Masu Ƙarfi a Duniya

Masar da Afirka ta Kudu Kadai Suka Shiga Jerin Kasashen Afrika Masu Ƙarfi a Duniya
Masar da Afirka ta Kudu ne kaɗai kasashen Afrika da suka samu gurbi a sabon jerin ƙasashen duniya mafi ƙarfi, lamarin da ke nuna ci gaba da tasirinsu a harkokin ƙasa da ƙasa.
Rahoton Best Countries Index 2026, wanda Makarantar Kasuwanci ta Wharton ta Jami’ar Pennsylvania ta fitar tare da haɗin gwiwar U.S. News & World Report, ya nuna cewa Masar ta zo ta 29 a duniya da maki 14.3 na ƙarfin tasiri, yayin da Afirka ta Kudu ta kasance ta 31 da maki 13.7.
Rahoton ya dogara ne da ra’ayoyin mutane 15,131 daga ƙasashe 33, inda aka auna yadda al’umma ke kallon tasirin ƙasa a duniya, ba wai ƙarfin soja ko tattalin arzikinta kai tsaye ba.
Abubuwan da aka yi la’akari da su wajen wannan ƙididdiga sun haɗa da ƙarfin tattalin arziki, tasirin siyasa, ingancin shugabanci, ci gaban fasaha da kuma matsayin ƙasar a idon duniya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted